Da dumi’dumi: ‘Yan ta’addan Boko Haram sun Kaiwa Gwamna Mai Mala Buni Hari sun kashe Dan Sanda daya tare da jigata mutun shida
Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun yi wa tawagar jami’an tsaron jihar Yobe kwanton bauna a ranar Asabar din da ta gabata, inda suka kashe dan sanda daya tare da jikkata wasu shida.
An kai harin ne a hanyar Jakana zuwa Mainok a jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa tawagar jami’an tsaron sun raka gwamnan Maiduguri ne domin halartar taron karo na 24 na jami’ar Maiduguri, inda aka baiwa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima digirin girmamawa.
Yayin da tawagar ta koma Yobe, an ce Buni ya tsaya a Maiduguri kafin tafiya Abuja don wata ganawa a hukumance.
Da yake tabbatar da harin, mai magana da yawun gwamnan, Mamman Mohammed, ya ce jami’an tsaron sun yi taho-mu-gama.
Sun yi wasu harbe-harbe amma jami’an tsaron da suka yi wa motocin gwamnan rakiya zuwa Damaturu sun yi musayar wuta da su, amma ‘yan sanda uku sun samu raunuka,” inji shi.
Ya ce jami’an tsaro sun samu nasarar dakile harin kuma wadanda suka jikkata suna karbar magani.
Sai dai wata majiyar tsaro daga ayarin motocin ta shaida wa wakilinmu cewa “dakarun da ke jagorantar ayarin motocin dauke da MRAP, Motar Bindiga, da wata motar da ke jigilar ‘yan sanda da DSS
Sakamakon haka sojojin sun mayar da martani da kakkausan wuta, lamarin da ya tilastawa ‘yan ta’addan ja da baya. Sai dai abin takaicin shi ne, dan sanda daya ya mutu, har ma sojoji biyu da suka hada da direba, ‘yan sanda uku, da kuma DSS daya suka samu raunuka.
“Jami’an tsaro sun dawo Damaturu, babban birnin jihar Yobe lafiya, yayin da aka kwashe wadanda suka jikkata da direban motar zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba, amma wasu daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali,” inji majiyar.
Ba a tabbatar da adadin wadanda suka rasa rayukansu daga bangaren ‘yan ta’addan ba har zuwa lokacin da aka buga labarin.