Labarai

Da dumi’dumi: ‘Yan ta’addar Boko Haram sun kashe wasu mutun Sha daya 11 a wani sabon hari da suka kai jihar Borno

Spread the love

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a kusa da Bale, wani kauye mai nisa a karamar hukumar Damboa ta jihar.

Wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun sare kawunan wasu mutane guda 11 a karamar hukumar Damboa da ke jihar Borno.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a kusa da Bale, wani kauye mai nisa a karamar hukumar Damboa ta jihar.

Kamar yadda majiyrmu ta ruwaito, majiyoyin ‘yan banga na yankin sun ce an gano gawarwakin wadanda lamarin ya rutsa da su a wurin da misalin karfe 5 na yamma.

Eh, an samo gawar mutane shida daga wurin da lamarin ya faru a yammacin jiya (Litinin) An same su a cikin wani tafki na jini domin an yanyanke sassan jikinsu gunduwa-gunduwa.

“Mun yi jana’izar su da yammacin yau kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Ko da yake mutane biyar sun bace, ba mu san ko sun tsere ko kuma an sace su ba,” in ji wata majiyar ‘yan banga.

Wani jigo a kungiyar ‘yan banga ya bayyana cewa, wa yanda al’amarin ya rutsa dasu na aiki ne a wurin da suke aikin gawayi inda Yan Ta’addan suka rutsa dasu inda ya kara da cewa mutane shida ne suka mutu nan take.

Majiyar ta ce, “Sun zo a kan rakuma suka kewaye mu, kamar sun Kai mutun 15. Na yi gudu da sauri, suka bi ni.

Abin farin ciki, na saba da filin; haka na tsere.

“Daga baya, mun tattara muka je wurin da lamarin ya faru. Sai ga gawarwaki shida a wurin amma ba mu ji ta bakin sauran mutane biyar ba.

“A safiyar yau an sake gano karin gawarwaki biyar don haka muna da gawarwaki guda 11. Ya zuwa yanzu sojoji da ’yan banga suna yankin a yanzu” inji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button