Labarai

Da dumi’dumi: Zanga-zanga ta barke a jihar Nasarawa, kasuwanni sun rufe bayan da kotun koli ta tabbatar da Sule a matsayin gwamna.

Spread the love

Wasu mazauna garin Lafia babban birnin jihar Nasarawa sun yi zanga-zangar nuna adawa da sakamakon hukuncin kotun koli da ta tabbatar da zaben gwamna Abdullahi Sule.

Daya daga cikin hanyoyin da masu zanga-zangar suka tare ita ce hanyar Lafia zuwa Jos inda suka kona tayoyi tare da rera taken nuna adawa da gwamnati.

An dai bayyana cewa an yi gaggawar rufe shaguna da cibiyoyin kasuwanci da makarantu a yankin domin kare rayuka da dukiyoyi.

Mikiya ta ruwaito cewa a yau Juma’a kotun kolin Najeriya ta tabbatar da zaben Abdullahi Sule a matsayin gwamnan jihar Nasarawa.

Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, a hukuncin da ta yanke, ta warware dukkan batutuwan da aka zayyana domin tantancewa, kan jam’iyyar PDP da dan takararta, David Ombugadu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button