Da irin wannan mulkin da Buhari yake yi gwara irin mulkin Turawan mulkin mallaka __ inji Oladimeji Fadipe.
Wani mamba a kungiyar kare hakkin Yarabawa ta jihar Lagos dake kudancin Nigeria mai suna Oladimeji Fadipe yace da irin salon mulkin nan da Buhari yake gwara irin salon mulkin Turawan mulkin mallaka.
Oladimeji Fadipe yace abinda yasa ya fadi haka shine, ya lura sosai babu abinda mulkin shugaba Buhari ya haifarwa da Najeriya sai rarraba kawunan “yan kasar, yace a lokacin da Turawan mulkin mallaka suke mulkar Najeriya sunyita yin yadda zasu yi su hade kan ‘yan Najeriya su zama kasa daya al umma daya Wanda daga bisani suka samu nasarar faruwar hakan a shekarar 1914.
Amma shi kuwa shugaba Buhari tunda ya hau mulkin Najeriya a shekarar 2015 babu wani Abu dayake bijiro da shi illa abubuwan da zasu rarraba kawunan yan kasar, Oladimeji Fadipe yace ba ataba samun lokacin da yan uwan su yan Arewa suka dakatar dakai kayan abinci kudancin Nigeria sakamakon wani rikici daya faru tsakanin kudancin kasar da arewacin kasar ba Sai a lokacin nan da Buhari yake mulki, kuma duk yadda yake tafi da salon mulkin Sa ne ya haifar da haka, saboda rashin saurin daukar mataki akan wata matsala data taso cikin gaggawa saidai kawai ya zuba ido har sai barnar ta afku.
Oladimeji Fadipe yayi wannan jawabi ne bayan da suka kammala wata ganawa da wasu shugabannin hausawa yan Arewa mazauna kudancin Nigeria game da yadda za a shawo kan matsalar data faru tsakanin yan kudancin Najeriyar da masu kai kayan abinci kudancin kasar.
Daga Kabiru Ado Muhd