Tsaro

Da izinin Allah Zamu cirewa duk wani jami’in tsaro kakinsa ko waye idan yace zai mana rashin Gaskiya a zabe ~Cewar Gawuna

Spread the love

A cikin wani bidiyon an hango mataimakin gwamnan jihar Kano Kuma Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyar Apc Dr Nasiru Yusuf Gawuna Yana Gargadi ga Jami’an tsaro harma yayi Barazanar cewa Idan Jami’an tsaron Basu kula zasu sa mutun ya rasa kakinsa.

A bayaninsa Gawuna Yana Mai cewa Kuma maganar Jami’an tsaro wallahi Babu wanda ya Isa yazo yanzu yace ga Abu na rashin Gaskiya zai goyi bayansa da izinin Allah zamu yi Masa sanadin kakinsa ko waye shi ya tsaya ya tsare Gaskiya Bamu mu yayi mana rashin Gaskiya ba Babu wanda mukace yazo ya kare ko ya Hana wasu suyi zaben su kowa abarshi yayi zabensa mutane Kuma ansan cewa munfisu mutane.

Dr Nasiru Yusuf Gawuna yayi kaurin suna wajen iya tsara kalamai musamman a bangaren nuna kusanci da Allah wanda Yan Adawa suke kallon hakan Wani salo ne na yaudara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button