Da sanyin safiyar yau Alhamis ne Rasha ta kai hari ta sama kan birnin Kyiv na kasar Ukraine, hare-haren sun zo ne a daidai lokacin da Kyiv ke cewa tana shirin kai wani gagarumin farmaki kan dakarun Moscow.
An Kashe Mutane Uku A Wani Harin Kasar Rasha A Kan Kiev
Hare-haren sun zo ne a daidai lokacin da Kyiv ke cewa tana shirin kai wani gagarumin farmaki kan dakarun Moscow.
Da sanyin safiyar Alhamis ne Rasha ta kai hari ta sama kan birnin Kyiv, inda ta kashe akalla mutane uku ciki har da wani yaro tare da kawo sabon firgici a birnin bayan shafe mako guda ana kai hare-hare.
A baya-bayan nan ne dakarun Moscow suka kaddamar da wasu hare-hare ta sama kan babban birnin kasar Ukraine, ciki har da wani harin da ba a saba gani ba da rana a ranar Litinin wanda ya sa mazauna yankin tserewa neman mafaka.
Harin na ranar Alhamis ya fara ne da misalin karfe 3:00 na safe agogon GMT, lokacin da aka tura jirage da makamai masu linzami kan birnin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku tare da jikkata wasu 12, in ji jami’ai.
“A cikin gundumar Desnyanskyi: mutane uku sun mutu, ciki har da yaro daya (an haife shi a 2012) kuma mutane 10 sun ji rauni, ciki har da yaro daya,” in ji Hukumar Soja ta Kyiv City a kan Telegram.
“A cikin gundumar Dniprovskyi: mutane biyu sun ji rauni.”
Rahotannin da suka gabata a hukumance sun ce an kashe yara biyu a harin.
A yankin Belgorod da ke yammacin Rasha, akalla mutane biyu ne suka jikkata a safiyar Alhamis a wani hari da aka kai a garin Shebekino da aka dora alhakin akan sojojin Ukraine, in ji gwamna Vyacheslav Gladkov a tashar Telegram.
“Wannan daren ya sake tada jijiyoyin wuya ga Shebekino. Sojojin Ukraine sun yi ta luguden wuta a birnin na tsawon sa’a guda,” in ji shi.
A baya dai Gladkov ya ba da rahoton cewa an kai hare-hare a garin wanda ya raunata mutane hudu.
A ranar Talata, an kashe mutum daya tare da jikkata wasu biyu a wani harin da aka kai a wata cibiyar ‘yan gudun hijira a yankin. Hakazalika an kai hari a gidajen man fetur da dama a ‘yan makonnin nan.
Hare-haren sun zo ne a daidai lokacin da Kyiv ke cewa tana shirin kai wani gagarumin farmaki kan dakarun Moscow.
AFP