Labarai

Da sanyin safiyar yau Litinin ne Matasa a Minna ta Jihar Neja suke Gudanar da zanga zangar Lumana kan Matsalar Wutar Lantarki.

Spread the love

Lamarin yanzu haka yana faruwa ne a Dai dai Shatale talen Kpakungu Wanda ya hada Hanyar Minna zuwa Legas a Cikin kwaryar Minna dake Karkashin Karamar Hukumar Chancaga ta Jihar Neja.

Lamarin ya Farune bayan da ‘Yan Nepa Suka Shiga Anguwar Soje-A a Nan Kpakungu da zummar karbar kudin wuta, sai matasan Anguwar suka koresu, dalilin haka `Yan Nepan suka Sauke Wutar Anguwar daga Transporma har tsawon kwanaki hudu basuda wuta, hakan ya sanya matasan Suka tsunduma zanga zangar lumana yanzu haka.

Matasan dai basu tada hayaniya ba, sai dai sun kulle babbar Hanya da ta hada Minna zuwa Legas, da Barikin Saleh Zuwa Babbar Kasuwar AA Kure Market Minna.

Sai dai An kawo Jami’an Tsaro Kala kala An Jibge a wajen Suna kallon kallo da masu Zanga zangar.

Sakataren Gwamnatin Jihar Hon. Ahmed Ibrahim Matane da Shugaban Karamar Hukumar Chancaga Hon. Abubakar Ibrahim Lalalo sun Halarci Wajen yanzu Haka.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar CP. Abubakar Usman ya samu zuwa wajen Inda Yace Matasan Su bude hanya za’ a biya musu bukatar su, Amma matasan basu buda hayar Ba.
Sai dai Yanzu haka ga Sojoji Sun Iso daga Tradoc Barrack dake Minna.

Jaridar Mikiya ta yi magana da Masu zanga zangar Daya daga cikinsu Musa Ibrahim yace “‘yan Nepa sun renamana hankali tun kafin a yanke mata wuta suna bamu wutane Na Awanni biyar cikin awanni 24 sannan Suna biyan Kudin wuta amma sai kawai domin wani Layi sunyi Hayaniya dasu kawai sai Su Sauke Layin dukkan Unguwar,

“Bukatar mu gwamna yasan Abinda Nepa suke mana, Ba Bukatarmu Hayaniya ko Rigima ba.

Sai dai Sakataren Gwamnatin Jihar yace Matasan suyi hakuri zasu zauna da Masu wutan.

Har kawo yanzu haka masu zanga zangar suna nan sunyi zaman Dirshan a wajen.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button