Tsaro

Da Yawan ‘Yan Gudun Hijira Sun Shiga Harkar Safarar Miyagun Kwayoyi Kuma Sun Yi Barazanar Shiga Boko Haram.

Spread the love

Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa ‘yan Gudun hijira da mayakan Boko Haram suka raba da muhallansu da suke sansanonin gudun hijira na Kuchingwaro da Durumi dake Abujar sun yi barazanar shiga kungiyar Boko Haram mudiin gwamnati ta ci gaba da rashin kulasu da kuma baiwa Tubabbun Boko Haram kulawa me kyau.

Sun bayyana hakane a wajan wani taro da aka yi a Abuja dake duba irin halin da suke ciki da kuma matakin da ya kamata a dauka akan hakan. Daya daga cikin ‘yan gudun hijirar dake Kuchingwaro, wanda ba ya so a boye sunansa ya gayawa Vanguard cewa basa jin dadin yanda gwamnati ke baiwa Boko Haram kulawa.

Yace tallafin magungunan da ake basu kyauta a baya an daina, yanzu saidai su sayar da kayan abincinsu ko wasu kayansu su sayi magani. Yace hakanan gashi mutanen gari suma suna nuna musu kyama. Yace akwai sanda wani dan kasar jamus ya so ya tafi dashi kasarsu amma da yaje ofishin jakadancin kasar Jamus na Najeriya sai suka hanashi Visa saboda shi dan gudun hijirane.

Yace amma suna kallo gwamnati ke baiwa wadanda ake kira da tubabbun ‘yan Boko Haram kulawar data kamata. Yace to idan shiga Boko Haram zai sa suma su samu irin wannan kulawar to zafa su shiga. Shima wani daya fito daga sansanin gudun hijirar Durumi ya bayyana cewa da yawa ‘yan gudun hijirar sun shiga harkar safarar miyagun kwayoyi saboda basa samun kulawa.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button