Kasuwanci

Da Yiwuwar A Rage Farashin Man Fetur A Wannan Watan.

Spread the love

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta cire hannunta daga tsarin rage ko kara farashin mai.

Shugaba Buhari ya ce san ba zai sake biyan tallafin mai ba.

Kamfanin kasuwancin kayayyakin arzikin man fetur PPMC na iya rage farashin man fetur wannan watan, Kamar yadda Jaridar The Nation ta ruwaito.

A hira da mataimakin shugaban kungiyar yan kasuwan man fetur masu zaman kansu IPMAN, Alhaji Abubakar Maigandu, ya bayyana cewa yan kasuwan na kyautata zaton za’a rage farashin man a watan Oktoba.

Ya bayyana hasashensa ne bisa ga saukar farashin mai a kasuwar duniya. Farashin yanzu ya sauko $39.38.

Amma ya ce sai kamfanin PPMC ta sanar da sabon farashin zasu fara sayarwa.

Amma hukumar lura da farashin man fetur PPPRA a watan Satumba ta ce ba farashin mai a kasuwar duniya kadai za’a duba wajen rage ko kara farashin a nan gida ba.

Idan baku manta ba gwamnatin tarayya ta cire tallafin mai a watan Maris na shekaran nan.

A watan Satumba, PPMC ta sanar da farashin man fetur da za’a sayarwa yan kasuwan mai a N151.56 ga lita, amma ta ki fadin farashin da su yan kasuwan zasu sayarwa yan Najeriya.

Saboda haka, yan kasuwan a fadin tarayya suka fara sayar da man tsakanin N158 da N162 ga lita.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button