Da Zuciya Daya Muka Cire Tallafin Fetur Ba Kamar Gwamnatocin Baya Ba~Gwamnatin Buhari.
Fadar shugaban kasa – “Da Zuciya daya muke cire tallafin mai a Nigeria, ba kamar gwamnatocin baya ba”
Daga Bappah Haruna Bajoga
Fadar shugaban kasa ta kare shugaba Buhari akan cire tallafin mai wanda ya zama silar kara farashin litar man a cikin kasar, fadar tace Gwamnatocin da suka wuce basa bada himma wajen daukar matakan cire tallafin, fadar ta kuma bayyana alfanun cire tallafin musamman ma wajen yaki da dabi’ar cin hancin daya kassara lamuran kasar.
.
A duk lokacin da aka kara farashin mai a Nigeria talakawan kasar suna nuna rashin jin dadin su tare da bayyana irin yadda hakan zai shafi rayuwar su ta yau da kullum wacce gwamnati bata yin ababen da suka bayyana da zasu kawo musu sassauci, kungiyoyi a kasar ma sun nuna damuwar su akan kara kudin man tare da bayyana cewa yanzu ma talakawa basu fita daga radadin karayar tattalin arzikin su da corona ta zama sila ba, ga radadin ayyukan ta’addanci, ga ambaliya, da sauran su.