Siyasa

Da’alama allah ya ke jaraftar Malam Pantami

Spread the love

Daga Jamilu Sama’ila Dandana

Babban Malami Sheikh Isah Ali Pantami, Wanda yake ya shahara a Gabatar da Karatuttuka na Addinin Musulunci, kuma Mabiyin Fahimtar Izala Ya shiga Cikin Jarabawar ubangiji.

Babu Shakka Duk Mutumin Daya dade Yana kalubalanatar Wasu mutane kokuma Wani Aiki Wanda Mutane ke suke Aiwatarwa, Idan Ubangiji yaso Saiya Jarabaeshi da Shiga Cikinsu.

Kowa Yasani Malam Pantami Yayi Kaurin suna wajen Suka da Kuma Nuna gazawar Shuwagabannin Tareda Kushe Irin yadda malamai ke Shiga Siyasa da Kuma Neman Mulki.

Allah cikin Ikonsa da Kuma Hikimarsa Saiya Jarabaeshi da Zama Minista a Rubabbar Gwamnati Irinta Shugaba Muhammad Buhari, Wadda ta Gagara yiwa talakkawa komai, sanann ta Lalata Komai a Nijeriya.

Wannan Hikimace ta Allah, Sannan Jarabawace ta Allah Madaukakin Sarki, Kuma izinane ga Sauran Malamai Sudaina Zafafa Sukarsu ga Masu Mulki Domin Kuwa Zasu iya xamowa daga Cikinsu.

Malamdai yayi Suka, Ankuma Nadi Murya da Kuma Hotuna Masu Motsi, Sannan dolene a Ringa Fiddowa Domin tunawa Malam.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button