Labarai

Dadaddiyar dangantaka da abokantaka ta da Oba na Legas ta taka rawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaban jihar Legas da kasa baki daya~ Buhari.

Spread the love

Buhari ya kira Oba na Legas.

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis ya kira Oba na Legas, Rilwanu Akiolu, don isar da gaisuwa a gare shi kan bikin cikarsa shekaru 77 da haihuwa.

Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Buhari, ya fadi haka a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa shugaban ya sake jajantawa da basaraken kan rikice-rikicen baya-bayan nan da ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi a Legas.

“Shugaban ya tuna da dadaddiyar dangantaka da abokantakarsa da Oba kuma ya yaba da rawar da wannan ta taka wajen samar da zaman lafiya da ci gaban jihar Legas da kasa baki daya,” in ji Shehu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button