Labarai

Daga karshe dai An rufe gidan Abincin N30 da ministan noma ya bude A Kano

Spread the love

An rufe Gidan cin abinci na N30, shahararren Gidan Abincine ne da Aka budeshi bayan maganar ministan noma Sabo na NoNo, Anaci Ana ‘koshi A N30.

saboda tsadar kayan masarufi da sauran Kayan hadin Abinci
Gidan cin abincin ya fara shahara ne a shekarar da ta gabata biyo bayan martanin da Ministan Noma, Sabo Nanono, wanda aka ruwaito cewa ya ce, “da abin da bai kai N30 ba,” mutum na iya samun abinci mai kyau ” .
An kafa gidan abincin N30 a Kano
Don tallafawa furucin na ministan, wani mazaunin Kano, Haruna Injiniya ya yanke shawarar kafa gidan abincin ne inda ake sayar da farantin abinci kan N30 inda ake sayar da shinkafa da wake da garri.

A makon da ya gabata, wakilinmu ya ziyarci gidan abincin Haruna da ke Layin Kuka, yankin Sani Mai-nagge a cikin jihar Kano sai kawai ya same shi a kulle.

Da yake zantawa da wakilinmu Haruna, wanda tuni ya koma tsohuwar sana’arsa ta gyaran kayan lantarki, ya ce an tilasta masa rufe gidan abincin ne saboda hauhawar farashin kayan abinci.

“Ci gaba da gudana a gidan abincin ba zai yiwu ba saboda hauhawar farashin kayan abinci.

“Lamarin ya canza saboda wani ma’aunin garri da muke saye a N200 yanzu ya koma N600, mudun shinkafa da a da ta zama N400 yanzu ta zama N1,300 kuma farashin kayan Miya ma ya tashi. An kafa kasuwancin ne don tallafawa gajiyayyu da marasa karfi amma hakan ba zai yiwu ba kuma, ”inji shi. Haruna Mai Gidan Abinci N30

Ya kara da cewa “Ina kira ga shugaban kasa da ya duba halin da ake ciki, talakawa suke fuskantar wahalar ciyar da kansu a wannan lokacin,”

Haruna ya ce lamarin ya kara ta’azzara ne sakamakon kulle-kullen da ya biyo bayan cutar ta COVID-19 wanda ya sa abubuwa suka yi wuya. Daga Abdulrashid Abdullahi,Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button