Labarai
Trending

Dala da ke mayarda wasu Hamshakan Attajirai a cikin dare yanzu Shugaba Tinubu ya kawo karshen hakan ~Kashim Shettima.

Spread the love

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana kwarin guiwar yadda darajar kudin Najeriya, Naira, ke gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwannin hada-hadar kudi, yana mai cewa za ta kara daraja yayin da Dala ke ci gaba da faduwa.

Ya ce dole ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kawo karshen tallafin man fetur da kuma tabbatar da hadewar kudaden musaya da bawa wasu dama da daddare su zama hamshakan attajirai.

VP, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a a lokacin da tawagar kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas (LCCI) karkashin jagorancin shugabanta, Gabriel Idahosa, suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa da ke fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja, a wata sanarwa da ya fitar ta hannun sa. Mai taimaka wa kan harkokin yada labarai, Stanley Nkowcha,

ya bayyana cewa wasu sun san kalubalen Amma Kuma har yanzu suna zagaya cikin kasar suna Yada Farfagandar duk da suna sane da cewa shugaba Tinubu ne ka iya magance wannan kalubalen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button