Dalibai mutun 375 da Sanata Uba Sani ya dauki nauyinsu Sakamakonsu ya fito Kuma yayi kyau.
Kuna iya tunawa Cewa A ranar 13 ga watan Janairun Shekarar 2020, Uba Sani Foundation, mallakin Sanata Uba Sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya suka dauki nauyin biyan kudin rubuta jarabawar WAEC na mutun 375 kyauta Ga ‘ya ‘yan talakawa Wanda Gidauniyar ta Biya Kudin Rajistar WAEC / ga wa’yanda suke da matakin SSCE.
Wannan tallafin da Sanatan ya gabatar ba’a saka Siyasa a ciki ba domin Sanata Uba Sani yabawa Arc Abubakar Rabiu Abubakar umarnin cewa yaje makarantu a nemo masa yaran talakawa masu kokari, ayi masu jarabawa a zabo wanda suka fi kwazo a cikin su, da niyyar zai dauki nauyin mutun 350 ya biya masu WAEC ko NECO
Arc Abubakar yaje yabi makarantun gwamnati cikin kananun hukumomi bakwai da sanatan ke wakilta ba tare da kowa ya sani ba Cikin sirri Gudun kar’a siyasantar da Al’amarin bayan An zabo daliban.
Sanatan ya Cika Alkawarinsa ya Kuma biya kudin Haka Kuma daliban sunje sun Zana jarabawar Kuma Allah yayi taimako Sakamakon Jarabawar ya fito Kuma yayi kyau matuka Hakan yasa iyayen yaran ke faman aika Sakon godiya ga Sanatan..
Sanata uba sani dai Yana Daya ko sahun Gaba Gaba daga Cikin sanatocin da Suka shahara a Majalisar dattijan Nageriya wajen Taimakon Al’ummar da suke wakilta musamman a bangaren Samar da jari ga masu koyon sana’o’i kala kala…