Dalibai Suna Fara Rubuta Jarrabawar WAEC A Makarantar Chibok.
Ɗalibai na rubuta jarabawar WAEC a makarantar Chibok
Dalibai a garin Chibok na jihar Borno sun fara rubuta jarabawar kammala sakandare a karon farko tun bayan da mayaƙan Boko Haram suka sace ‘ƴan mata sama da 200 a shekarar 2014.
Ɗauke ‘ƴan matan da Boko Haram tayi ya ja hankalin duniya inda aka ƙaddamar da fafutikar neman a dawo da su.
Iyaye da malaman makarantar Chibok sun shaidawa BBC cewa sun ji daɗi da suka ga ‘ƴa’ƴansu suna rubuta jarabawar a kusa da gida.
A tsawon shekaru da aka shafe, sai dai ɗalibai su yi tafiya mai nisa domin rubuta jarabawar a garin Maiduguri wasu kuma har zuwa garin Jos.
Ɗalibai 238 ne ke rubuta jarabawar ta WAEC a makarantar sakandaren Chibok.
A daidai wannan lokacin ne da ɗaliban ke rubuta jarabawar, aka sace su shekaru shida da suka gabata.
An ɗauki tsauraran matakan tsaro a makarantar. Ɗalibai da malamai ne kawai aka amince su shiga makarantar bayan jami’an tsaro sun tantance su.
An rufe makarantar Chibok a 2014 bayan Boko Haram ta sace ɗaliban makarantar sama da 200.
Sace ɗaliban ya ja hankalin duniya da manyan masu faɗa a ji ciki har da uwar gidan shugaban Amurka Michelle Obama inda ta yi kiran a kuɓutar da su.
Har yanzu akwai sama da ɗari daga cikin ɗaliban da ba a gano ba.
Daga Amir sufi
Aƙalla mutum 37,000 ake tunanin an kashe yayin da aka raba sama da mutum miliyan biyu da rabi da gidajensu a shekaru sama da 10 na rikicin Boko Haram.