Labarai
Daliban da aka sace a Makarantar kagara ba zamu biya ‘yan ta’adda kudin fansa ko sisi ba ~Gwamna Lolo
Gwamna Abubakar Sani-Bello na jihar Neja ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta biya kudin fansa ga masu satar yaran makarantar ta Kwalejin Kimiyyar Gwamnati da ke Kangara, karamar hukumar Rafi ta jihar ba.
Mista Bello ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Yau Ranar Laraba, bayan sace wasu dalibai da ma’aikatan Kwalejin a daren Talata.