Siyasa

Dalilin da ya sa na ki zabar kowane dan takara a lokacin zaben fidda gwani na shugaban kasa na APC – Buhari

Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa bai fifita kowani dan takarar shugaban kasa ba a lokacin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki.

Shugaban ya ce ya koyi darasi daga abubuwan da ya faru a baya yayin da ya kasa zama shugaban kasar har sau uku har sai an yi yunkurin na hudu ta hanyar dimokuradiyya.

Buhari ya ce kin nada kowane dan takara ya ta’allaka ne kan yadda ya “kara zaben shugaban kasa har sau uku kuma ya kare a kotun koli ba tare da nasara ba, sai dai ya yi nasara a karo na hudu ta hanyar dimokradiyya.

Shugaban ya yi wannan jawabi ne a garin Lafia yayin taron tunawa da Sir Ahmadu Bello na shekara ta 2023 wanda gwamnatin jihar Nasarawa tare da hadin gwiwar Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation suka shirya.

Shugaban ma’aikatan fadar sa, Ibrahim Gambari ne ya wakilce shi, inda ya bukaci al’ummar Najeriya da su amince da sakamakon zaben 2023.

Ya kuma yi kira ga ‘yan takarar da ba su gamsu da su ba da su nemi hakkinsu a kotu.

Ya ce Ahmadu Bello ya jajirce wajen ganin an samu hadin kai da zaman lafiya da ci gaban Najeriya kuma ya tsaya tsayin daka har zuwa rasuwarsa.

Shugaban ya roki ‘yan Najeriya da su rungumi sadaukar da kai da kuma abubuwan da ya bari.

Related Articles

One Comment

  1. Do you need targeted Customers from social media , if yes I am here to help you check out my Fiverr 5 stares profile serving over 880 happy customers in which I can create attractive social content for any industry

    contact me here and tell me what you need ===== > https://tinyurl.com/ycktwuxh

    See you there

    Regards
    Shirley

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button