Labarai

Dalilin Da Yasa Ba Zamu Iya Bincikar Yan Majalisar Dake Da Hannu A Waken Karban Kwangilar NDDC Ba~Majalisa.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Kwamitin dake kula da bin ka’idar aiki na majalisar Dattijai ya bayyana cewa dalilin da yasa ba zai iya bincikar ‘yan majalisa da ake zargi da hannu a karbar kwangiloli a maaikatar kula da yankin Naija Delta ta NDDC ba shine saboda babu isassun bayanai akan lamarin.

Ministan ma’aikatar, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana sunayen ‘yan majalisar inda yace an basu aikin kwagilar wanda an biya wani kaso daga ciki amma sun yi watsi da aikin ba tare da an kammala ba.Mun kawo muku cewa wasu daga cikin ‘yan majalisar sun karyata ikirarin na sanata Akpabio saidai duk da haka majalisar ta kafa kwamiti na musamman akan wannan lamari.

Sanata Ayo Akiyeleru wanda shine ke kula da harkar binciken ya bayyana cewa basu samu isassun bayanan da za su yi binciken akai ba. Dalili kenan da yasa basu binciki ‘yan majalisar da ake zargi ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button