‘Dalilin da yasa satifiket ɗina na WAEC ke dauke da sunan Sadiq Abubakar’ – Atiku ya mayar da martani kan zargin jabun takardu
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana rashin daidaiton da ya samu a jarrabawar sa ta babbar Sakandare, SSCE.
Atiku ya yi wannan karin haske ne ta bakin Dele Momodu daya daga cikin masu taimaka masa a ranar Talata a wani sako da ya wallafa a dandalinshi na sada zumunta, X.
A cewar Momodu, wannan bayanin ya zama dole ne biyo bayan zargin da ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki ke yi na jabun takardun makarantar.
Wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC sun tuhumi sunan “Sadiq Abubakar” a cikin takardar shaidar kammala jarabawar WAEC na Atiku sabanin sauran takardun shaidarsa.
Sai dai Momodu ya ce ya mika wadannan zarge-zargen ne ga tsohon mataimakin shugaban kasar, wanda shi ma ya bayar da amsar sabanin.
Momodu ya rubuta cewa, “Wasu ’yan jam’iyyar APC sun rika yi mani boma-boman tambayoyi da zargin yin jabun makarantar, ALHAJI ATIKU ABUBAKAR (GCON), wanda nan da nan na tura masa, ga kuma amsar da ya bayar: “Eh na yi amfani da Sadiq Abubakar wajen zana WAEC dina, kuma bayan na ci jarrabawa na je na rantse da rantsuwar cewa ni mutum daya ne, da Atiku Abubakar na je ABU a matsayin Atiku Abuakar na ci jarrabawa a matsayin Atiku Abubakar. Hukumar da’ar ma’aikata ta tarayya ta yi hira da Atiku Abubakar kuma ta dauke shi aiki a Hukumar Kwastam a matsayin Atiku Abubakar. To ina jabun a can?’ – ATIKU ABUBAKAR
“Jam’iyyar APC ta social media za ta iya tura tarin tambayoyin da ake yadawa ga maigidan nasu tare da samun amsa kai tsaye…