Labarai
Dama Can Ni Mai Kudi Ne Kafin Ka Bani Mukami Ministan Shari’a, Abubakar Malami Ya Gayawa Shugaba Buhari.
Daga Comr Yaseer Alhassan
Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya bayyanawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa dama can shi me kudi ne tun kafin shugaban kasar ya bashi mukamin Minista.
Malamai ya aikewa da shugaban kasa wannan bayani ne saboda yanda wasu ke ta kira a tuhumeshi kan Almundahanar Miliyoyin Kudi.
A cikin takardar bayanin da ya aikewa shugaban kasar, Malami ya bayyana cewa cikin bayanan da ya bayar kafin ya zama Minista ya saka kadarori 27 da ya mallaka.