Dan Majalisa a jihar kano ya magance Matsalar wutar Shekaru 40
Sama Da Shekaru arba’in 40 suna fama da matsalar wutar lantarki amma zuwan sabon dan majalisar ya magance Matsalar
bayan Hukumar wutar lantarki ta aminta shi kuma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR yakarbi Takardar Sahalewar Hukumar raba wutar Lantarki ta Kasa wadda ta amincewa bukatar da Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Bichi Hon Abubakar Kabir Abubakar Bichi ya shigar gareta don neman Mobile Transformer me karfin 1×30/40MVA, 132/33KV.
Gwamna ya nuna jindadinsa kwarai bisa wannan abu da Hukumar raba wutar lantarki ta Kasa tayiwa Karamar Hukumar Bichi da Jihar Kano baki daya tare da yabawa Dan Majalisar bisa namijin kokari dayayi don ganin wannan alheri yasamu a yankinsa.Sannan Gwamnan ya tabbatar da ceaa zai Halarci bikin karbar wannan Transformer wadda za’a kaita garin na bichi da zarar angama aikin gina tashar wutar wanda Dan Majalisar yadauki nauyin aikin.