Labarai
Dan Majalisar Wakilai Isma’il Maihanchi Ya Rasu
Zababben dan majalisar ya samu nasara a zaben 2023, inda ya tsaya takara a kan babbar jam’iyyar siyasa.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jalingo/Yorro/Zing a jihar Taraba, Isma’ila Maihanchi ya rasu.
Maihanchi ya rasu ne da sanyin safiyar Asabar bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Ya lashe zaben ne a karkashin jam’iyyar PDP.
Wata majiya daga dangin ta shaida wa gidan talabijin na Channels cewa za a binne gawarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada da rana.