Labarai
Dan Najeriya Akinwunmi Adesina Ya Sake Zama Shugaban Bankin Africa A Yau Alhamis.
Dan Najeriya, Akinwummi Adesina ya sake lashe zaben zama shugaban bankin Nahiyar Africa, Afdb. Zaben nasa ya tabbatane a zaben da bankin ke gudanarwa a yau Alhamis a Birnin Abidjan.
Hadimar shugaban kasa akan kafafen sadarwa, Laureta Onochie ce ta bayyana haka ta shafinta na sada zumunta yayin da take taya Adesina murna.
Adesina dai ya sha fama da zargin Aikata ba daidai ba inda hakan ya rika mai barazanar sake lashe zaben wanda har sai da aka gudanar da bincike na musamman akansa.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe