Rahotanni

Dan Sanda ya Tsallaka Gidana Ya Sacemin Naira 280,000~Otighan Sam.

Spread the love

Wani wanzami, wanda ya bayyana kansa a matsayin Otighan Sam, ya zargi wani dan sanda da ke aiki a rundunar ‘yan sanda ta musamman masu yaki da fashi da makami da ke jihar Ribas da fasa gidansa a ranar Juma’a da misalin karfe 12 na dare, inda suka lalata masa kadarorinsa, suka sace masa N280,000.

Lamarin ya faru ne a No 23 kan titin Nnewi, Mile 1 Diobu, Fatakwal, wani rahoto da jaridar PUNCH ta rawaito tace.

“Wanzami ya ce ya ga jami’in na SARS da bindigogi biyu; karamar bindiga da AK47, ya kara da cewa ya samu rakiyar wasu mutane biyu dauke da makamai.

Sam ya ce mai yiwuwa dan sandan yana tare da shi saboda tun farko ya ki biyan kudin kayan maye da yasha (dan sanda) da wasu abokansa suka sha a wata mashaya.

Ya ce, “Wani jami’in SARS dauke da bindigarsa kirar AK47, tare da wasu mutum biyu dauke da adduna sun zo gidana da misalin karfe 12 na dare, suka kutsa kai cikin gidan makwabta na suka fara dukansa suna tambaya inda dakina yake.

“Da ganin abin da ke faruwa, sai na yi kokarin guduwa saboda da gaske jami’in ya bugu kuma yana sa bakin bindigarsa yana barazanar harbe shi idan bai nuna masa dakina ba. Lokacin da jami’in da yaransa suka isa dakina, sai suka yi kaca-kaca da gidan baki daya, suka lalata kayayyakina kana suka tafi da N280,000 dina.

“Sunan dan sanda Usman, laifi na kawai shi ne na ki biyan kudin giyar da ya sha tare da abokansa saboda ba ni da kudi.”

Sam, ya ce ya kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda na Mile One kuma an gayyaci dan sanda da ake zargi don amsa tambayoyi.

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Nnamdi Omoni, ya ce har yanzu ba a ba shi labarin abin da ya faru ba.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button