
Daga Kais Dauda Sallau
Da ace lokacin yakin niman zabe ne Coronavirus ya zo, da ba shakka yan siyasa daga kowa ce jam’iya za su yi kokari gurin taimakawa al’umma domin su samu karbuwa.
Ba shakka akasarin yan siyasa ba wai suna kyautatawa mutane saboda Allah, kokuma saboda kishi ko tausayin mutanen ba, sai de saboda suna da wata bukatar da su ke son cimma a gaba.
Inda a ce yan siyasa suna kishin al’ummarsu da talaka ba zai tsinci kanshi a halin da ya ke ciki yanzun ba.
Bayan tallafin da zai fito daga gwamnatin tarayya, ka sake ware yan majalisun tarayya da na jihar.
Ace ko wanne daga cikinsu ya ware wani abu daga cikin abinda ya ke da shi domin tallafawa al’ummarsa, misali;
- Ko wani dan majalisar dattijai (dattawa) ya ware ma mazabarsa naira miliyon talatin (30m)
Dan majalisar wakilai ya ware ma mazabarsa naira miliyon ashirin (20m)
Dan majalisar jihar ya ware ma mazabarsa miliyon uku ko biyar (3-5m)
Gwamna ya ware ma ko wace karamar hukuma miliyon biyar (5m)
Gwamnatin tarayya ta kawo nata, ko wani minista ya kaiwa jihar sa guduma. Ko wani komishina ya kaiwa karamar hukumarsa na shi gudumawar, shugaban karamar hukuma ya ba da na shi gudumawar. Yan kasuwa masu karfi su kawo nasu, suma sarakuna su yi nasu kokarin.
Wallahi idan za’ayi haka, kuma a yi amfani da abinda aka samu ta yadda ya kamata, ba shakka talaka ba zai yi gaddama da zaman gida ba. Amma kawai ka rufe mutane a gida ba wani abin sarafawa, ai akwai matsala.
Duk ba dan siyasar da baifi karfin wannan kudin da na fada ba, sai dai su dinga ce muku ba kudi amma kuna ganin suna yin abubuwan kudi.
Yan kasuwa da bankunan da su ke taimakawa gwamnati da kudade ba su yi wa talakawa adalci ba, wannan kudaden talakawa ya kamata su rabawa, domin talakawa sun fi gwamnati niman taimako. Da yan kasuwar da bankunan duk sunsan yadda za su yi su zagulo talakawar da su ka cancanci taimako. Amma saboda suna son su kyara hanyarsu ne, sai suna baiwa gwamnati.
Da a ce lokacin yakin niman zabe Coronavirus ya zo;
- Da mun ga abinci na yawo ta ko ina daga ko wace jam’iya (yan siyasa).
- Da mun ga ana raba duk wani abin kariya daga kamuwa daga Coronavirus irinsu abin rufe baki da hanci, abin sawa a hanu da kuma sanadarin wanke hanu.
- Da mun ga ko wani dan siyasa daga ko wace jam’iya na iya kokari gurin rabawa al’umma kudade domin samun karbuwa.
Amma da ya ke dan siyasa dan jari hujja ne, duk lokacin da baya tsammanin samun wani abu kokuma baida bukata a gurin ka, toh ba zai taba yarda ya kashe kudin shi ba. Dole sai lokacin da ya ke da bukatar wani abu a gurin ka kafin zai fidda kudin shi ya kashe maka, domin yana tsammanin samun riba.
Amma tunda ba lokacin yakin niman zabe ba ne, ba abinda talaka zai gani sai wulakanci.
Ba za mu ce duka yan siyasa basu kishin al’ummarsu ba, akwai masu kishin al’ummarsu, amma mafi yawancin su ba al’ummarsu bane a gaban su. Kan su kawai su ka sani da yaransu.
Allah ya yaye mana. Allah ya kawo mana mafita.