Kasashen Ketare
Dan Tsohon Shugaban Kasa Zai Sha Daurin Shekaru Biyar.
Dan tsohon shugaban Angola zai sha daurin shekaru biyar
Kotu ta yi wa dan tsohon shugaban kasar Angola, Jose Eduardo dos Santos, daurin shekara biyar a gidan yari, bayan ta kama shi da yin almundahan.
An tuhumi Filomeno dos Santas ne da laifin satar dala miliyon dari biyar daga asasun ajiyar kudaden wajen kasar, wanda ya shugabanta daga shekarar 2013 zuwa 2018.
Shugaban kasar mai ci Joao Lourenso ya sha alwashin yaki da cin hanci a kasar, kuma binciken wasu daga cikin iyalan tsohon shugaban kasar. A shekarar 2017 ya sauke `yar tsohon shugaba dos Santos, wato Isabel daga shugabancin kamfanin man kasar, bisa zargin ta da almubazzaranci, amma ta musanta.
Daga Umar Gaya