Labarai

Dan Wasa Kwallo Ahmad Musa ya tsere daga Kulob dinsa na kasar Saudi Arabiya, Al Nassr,

Spread the love

Kyaftin din Kungiyar wasan Super Eagles ta Nageriya Ahmed Musa, ya raba gari da kulob din na Saudi Arabiya, Al Nassr, shekaru biyu bayan komawarsa kungiyar. Musa ya koma kungiyar ta Saudiyya ne a shekarar 2018 daga kungiyar Firimiya ta Ingila, Leicester City, kan yarjejeniyar shekara hudu. Duk da cewa saura shekara biyu kwantiraginsa ya kare, kungiyar ta sanar da barin tsohon tauraron ta Hanyar VVV Venlo a shafinsu na Twitter tare da gajeren bidiyo. Ba a ba da dalilin dakatar da kwangilar daga bangarorin biyu ba kawo yanzu.

”kungiyar ta ce a shafin ta na Twitter. Sanarwar ta tabbatar da rahotannin farko cewa dan wasan mai shekaru 28 na shirin barin kungiyar, wanda ya musanta hakan. Musa yana da alaƙa da komawa kulob din Fenerbahce na kasar Turkiya a wannan bazarar Tsohon dan wasan na Kano Pillars din ya Gaza zura kwallo ko daya a raga a wasanni 17 da ya buga a wannan kakar sannan kuma ya kalli yadda kulob din na Riyadh ya rasa kofin a hannun abokan hamayyarsa Al Hilal. A shekaru biyu da ya yi a kulob din, kyaftin din na Eagles ya ci Kofin Saudi Arabiya na 2019 kuma ya ci kwallaye bakwai a wasanni 24 da ya yi a kakar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button