Dana Haɗu Dakai, Dana Zabga Maka Mari Ganduje Ga Kwankwaso
Da fari da zaɓen gwamna a Kano yabar baya da ƙura ga Abdullahi Umar Ganduje, biyo bayan faɗuwan Gawuna
NNPP ta ƙwace Kano, Sannan daga Sama Dr Rabi’u Musa Kwankwaso nacigaba da rufe ƙofa da Shugaban Ƙasa Tinubu
NNPP na rushe rushen abinda ta kira aika aikan Ganduje, Kwankwaso na ƙara Haɗuwa da Shugaban ƙasa
Da alama tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje baiji daɗin sake haɗuwa da jagoran NNPP Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya sake yi da Shugaban ƙasa Tinubu ba.
Tsohon Gwamnan na Kano (Ganduje) yace tabbas da ace ya haɗu da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a wajen shugaban ƙasa, da saiya kafta masa ɗan karen mari a fuska.
Tsohon gwamnan yayi wannan kumfar bakin ne a wata ƙwarya ƙwaryan ganawa da manema labarai da yayi a Villa, jim kaɗan bayan shima Gandujen ya gana da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni da dama dai sunce, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gana da Tinubu ne akan nuna rashin jin daɗin sa da ruguje gine-gine daya kira ba bisa ƙaida ba da gwamnatin Abba Kabir Yusuf take yi a Kano.
To sai dai kuma, tuni gwamnatin ta jihar Kano ta ƙara jaddada burin da take dashi naci gaba da rushe rushen har sai baba tagani.
Daga hannu guda kuma masu sharhi a fagen siyasa na ganin magana ce kawai ta raha da Ganduje ya saba, duba da yadda wanda yake cewa zai mara ya kasance uban gidansa na lokaci mai tsawo a siyasa.
Yayin da wasu ke cewa, tsaf zai iya marin tunda jam’iyyar tsohon maigidan nasa ta kwaɗa ɗan takarar sa da kasa a zaɓen gwamnoni daya wuce.
Koma dai menene, fatan za’ai siyasa bada gababa, cikin mutumci da karamci.