Rahotanni

Dangote ya karawa Najeriya matsayi da martaba a duniya – Buhari

Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya yabawa fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Aliko Dangote, yayin da yake murnar cika shekaru 66 da haihuwa, tare da yi masa fatan Allah ya karo tsawon rai, lafiya da kuma shekaru masu albarka.

Shugaba Buhari ya yaba masa bisa dimbin kokarin da yake yi domin ci gaban kasa.

Shugaban kasar a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu ya fitar, an ruwaito cewa, “Ina taya fitaccen dan kasuwa Aliko Dangote murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

“Ya kara wa Najeriya daraja da kima a duniya. Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi karfi da hikimar da zai kara yi wa al’umma.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button