Dangote ya samu dala miliyan 575 a cikin awa 24
Hamshakin attajirin nan na Najeriya Aliko Dangote, ya samu karuwar arziki, inda ya samu kimanin dalar Amurka miliyan 575 cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
An lura da wannan gagarumin murmurewa a ranar Litinin, kamar yadda mujallar Forbes ta ruwaito.
Da arzikin da ya kai dala biliyan 10.5, hamshakin attajirin mai shekaru 66 ya nuna karuwar arzikinsa da kashi 5.82 cikin dari a cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Ya zuwa safiyar yau, dukiyar Dangote ta kai kusan dala biliyan 9.8.
Ana iya danganta wannan haɓakar da samun kashi 10% na hannun jarin Dangote Cement Plc yayin zaman ciniki na yau. Yunkurin ya biyo bayan sanarwar fara shirin Tranche I raba sayayya na kamfanin.
A baya dai an dawo da shirin hannun jari na Dangote Cement, wanda ya hada da sake siyan hannun jari har 168,735,593 da aka biya cikakke. Wannan yana wakiltar 1% na hannun jarin da aka bayar a halin yanzu. Hannun jarin simintin Dangote ya bude kasuwar ne a kan Naira 330.1 kan kowanne kaso, wanda hakan ya nuna tsawon mako 52.
A farkon rabin wannan shekarar, kamfanonin Dangote da suka hada da siminti, sukari, gishiri, gari, mai, da iskar gas da dai sauransu, sun samu dala miliyan 504 daga kasuwannin hannayen jari.
Sakamakon haka, dukiyarsa ta karu daga dala biliyan 4.9 a ranar 31 ga Disamba, 2022, zuwa dala biliyan 5.4 a ranar 30 ga watan Yunin 2023. Wannan ci gaban ya samo asali ne sakamakon karuwar kashi 10% na hannun jarin kamfanin Dangote Cement Plc a farkon rabin shekara.
Kamfanonin Dangote sun hada da Dangote Cement, Dangote Sugar, da NASCON. Ya mallaki kashi 85 cikin 100 na simintin Dangote da ake sayar da shi a bainar jama’a ta hannun wani kamfani.
Dangote Cement yana aiki a kasashe 10 a fadin Afirka kuma yana da karfin samar da metric ton miliyan 48.6 a duk shekara.
.