Dankari: Almajirai Dubu 35 Gwamnatin Kaduna Takora.
Gwamnatin Jahar Kaduna ta Kora Al’majira dubu 35 zuwa Jahohi 17….
Daga Ahmed T. Adam Bagas
Comishiniyar Jinkai da Inganta Rayuwar al’umma ta Jahar Kaduna Hajiya. Hafsat Baba ta Sanar da Hakan ga Ma’aikatan dillancin Labarai NAN a Kaduna.
Hafsat din tace Sun karbi Almajirai Dubu 1 yan asalin Jahar Kaduna daga wasu Jahohin Kasar Nan.
Har Ila yau Tace Ma’aikatarta da Hadin Guiwar Asusun Tallafawa Yara ta Duniya UNICEF ne zasu Cigaba da Kulada Iimin Yaran da Aka kawo daga Wasu Jahohin.
Kwamishiniyar Tace Gwamnatin Kaduna Ta dauki wannan Matakin ne Domin Inganta Ilmin Al’Qur’ani da na Zamani a Fadin Jahar.
Hafsat Tace bata yadda da Lafiyar Almajiran da aka kawo ba, Gwamnati zata killace su atabbatar da Ingancin Lafiyarsu Sannan a Hadasu da Takwarorin su -Inji Ta.
Bullar Cutar Covid-19 ce Ta sanya Gwamnoni suka fara Korar Almajirai zuwa Jahihinsu Na Asali.