Kasashen Ketare
Daular Larabawa Ta Aiko Da Tallafin Kayan Abinci Zuwa Najeriya.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Firayim Ministan Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, ya umarci jami’ai a kasarsa da su tura kayan agaji na gaggawa da kayan abinci zuwa Najeriya.
Ofishin jakadancin Hadaddiyar Daular Larabawa a Najeriya shine ya sanar da hakan a wani sakon Twitter.
Dangane da tallafin, Maktoum ya bayyana cewa, wannan na cikin yunkurin da kasar take na tallafawa Najeriya a kokarin da take na yaki da cutar Coronavirus.
Kayan sun hada da, Tan bakawai na kayayyakin kiwan lafiya, da kuma Tan biyar na kayan Abinci.