Rahotanni

Daurin Rai Da Rai, Ko Kashewa Shine Kawai Hukuncinda Ya Dace Ayiwa Masu Daukar Nauyin Tashe Tashen Hankula A Najeriya, Inji Aminu Waziri Tambuwal.

Spread the love

Gwamnan Jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya sharwaci Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, dakuma yan mahalisun Najeriya da su kafa wata doka da zata daukin kwakkwaran mataki kan masu daukar nauyin Kisan jama’a a sassan Najeriya.

Gwamna Tambuwal ya nemi Gwamnatin tarayya dakuma yan majalisu da su kafa Dokar da zatayi hukuncin Kisa, ko daurin rai da rai ga masu daukar nauyin sha’anin ta’addanci a Najeriya.

Tambuwal ya nuna shakkarsa kan cewa makaman da ke hannun wadannan Mutane kan iya zarce Wadanda suke hannun jami’an tsaro.

Gwamna Tambuwal hukuncin kisa ko daurin rai da rai itace kawai hanya daya ta samawa Najeriya zaman lafiya.

Gameda abunda ya faru a Jahar Sokoto na Kisan jama’ar Jahar, Gwamna Tambuwal yaci gaba da cewa suna daukan daukar matakai ta hanyar daukan yan banga da zasuyi aiki a sassan da ke fama da matsalar tsaro a Jahar.

Tambuwal ya Kara da cewa Wadannan yan banga zasu aiki kafada da kafada da jami’an tsaro a Jahar, don kaucewa Kada yan banga su dauki doka a hannunsu.

Gwamna Tambuwal ya bayyana cewa akwai karamcin ilimin addini a kawunan Wadanda sukayi wannan danyen aiki, Sannan ya bayyana cewa babu addinin da ya tanadi wannan lamari.

Daga karshe yayi Kira ga kungiyoyin addini da cewa su fadada da’awarsu zuwa kauyuka don fadakarda magoya bayansu.

Saboda shi dai ilimi kowa yasan ya tanadi zaman lafiya dakuma ci gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button