Daurin Shekaru 15 Da Wani Mahaifi Yayiwa Ɗansa Wanda Aka Ce Hafizi Ne A Gidansu Cin Zarafi Ne Da Rashin Sanin Darajar Dan_Adam.
Daga Kais Dauda Sallau
Wannan wani matashi ne wanda a ka ce Hafizi ne (mahaddacin Al-qur’ani) matashin dan shekara 31 ne dake zaune a unguwar Sheka, Kano. Wannan matashin mahaifinsa ya daureshi a gidansu har tsawon shekaru goma sha biyar (15yrs). Mahaifinsa ya daureshi ne bisa wasu dalilan da shi kadai ya sani.
Toh koma menene wannan bawan Allah ya yi wa mahaifin nasa bai cancanci wannan hukuncin ba, wannan rashin daraja dan_adam ne. Domin da ganin hoton wannan bawan Allah kasan baya samun kulawan da ya dace. Yau ko dabba ka kulle ba ka basa kulawa yadda ya dace, sai Allah ya tambaye ka balle mutum.
Wai ma a ina mahaifin wannan bawan Allah ya samu wannan hukuncin da aikata a matsayin hukuncin da addini ya zo da shi?
Ya kamata mutane su san yaran da su ka haifa amana ce gare su, kiwo Allah ya ba su, kuma zai tambaye su yadda suka kiwon ta yaran da ya ba su. Yadda uba ya ke da haƙƙi a kan dansa na ya yi masa biyayya da gyautatawa, haka ɗan ma yana da haƙƙi a gurin uban nashi. Saboda haka ya dace mu dinga mutunta junanmu. Ya kamata mu san dukkan mu muna da haƙƙin da za mu ba juna a matsayin ɗa da uba. Uba ya ba ɗa haƙƙin shi, ɗa ya ba uba haƙƙin shi.
Hukumar yan sandan jihar Kano ta ƙubuto da matashin ne bayan da ta samu rahoto akan lamarin, inda SP Baballo Majia da DPO din karamar hukumar Nassarawa suka jagoranci ƙubuto da matashin. Inda aka garzaya da matashin asibitin Nassarawa domin kulawa da lafiyarsa daga irin uƙubar da mahaifirsa ya gallaza masa.
Allah ya sa mu dace