Dausayin Masoya: Yadda So Ke Lalata Aure.
Daga Bukar Ali
Yana daga cikin abin da So ke ma dan Adam, shine ingiza shi zuwa ga auratayya, yawancin lokuta mutane kan kasance cikin mafarkin dawwama cikin yanayin shauki da suka tsinci kansu a lokacin da suka tsunduma cikin kogin So.
Irin shaukin So kan jefa mutane cikin mafarkin Irin soyayya ta tatsuniya, inda wani Yarima da wata gimbiya suka kare rayuwa cikin soyayya maras nakasu.
A irin wannan tunani muna hararo cewa ga dukkan wani saurayi akwai wata halitta ta jinsin mace wacce ta dace dashi ta kowane siga, wacce aka halittar ta domin sa, kuma kaddara ce su hadu da juna. To da zaran suka hadu suka tsinci kansu a cikin yanayi na shauki da kuma sha’awar juna sai su dauka sun hadu da mafarkin nasu.
Bayan aure sai su fahimci gaskiyar lamari cewa kowannen su ba goma yake ba, yana da tawaya a fannoni maban-banta, saboda haka tunaninsu na rayuwa da zamantakewa me cike da shauki da farin ciki sai ya fara samun tasgaro. Yadda suke boyewa juna nakasa kamin aure bai yiwuwa bayan auren.
Zargi da ganin laifi sai ya shigo, kowanne ya dunga ganin kamar yayi kuskure wurin zabin abin kaunar kuma abokin rayuwarsa.
A wannan gaba sai zabi ya zama biyu, rayuwa cikin yanayi na rashin gamsuwa da juna ko kuma rabuwar aure.
Duk yadda muka kalli abin, shi shaukin so kan jefa mu cikin tunanin cewa soyayya da shakuwa abu ne mai dawwama, tare da kallon abin son namu a matsayin kammalalle, shiko mutum tara yake.
Abin takaicin shine yawancin wannan kan jefa auratayya cikin garari.