Kimiya Da Fasaha

DG Kashifu Inuwa Jan Gwarzo.

Spread the love

DG KASHIF INUWA ABDULLAHI

TARISHIN SA DAKUMA NASARAR DAYA TAKA KAN JAGORANCIN HUKUMAR NITDA CIKIN SHEKARA GUDA.

Daga Hassan Nakudu

An haifi malam Kashif Inuwa Abdullahi a ranar 21/02/1980 matashi Daya zamo alfahari da abun shaawa a duk fadin duniya Musamman a fannin fasahar zamani, malam Kashif Inuwa yasoma karatunsa a makarantar primary ta hudu Islamiyya dake garin Hadejia Wanda Bayan ya kammala yakuma halarcin makarantar sikandire ta kimiyya da fasaha ta Garin kafin hausa inda yazama gwarzo Kuma haziki cikin Daliban dasukayi karatu a wannan makaranta cikin wannan shekara

Kashifu Inuwa Abdullahi kamar saura bai tsaya haka inda ya halarci makarantar Abubakar tafawa balewa daga shekarar 1999 inda ya kammala a shekarar 2003, babban Burin Kashif Inuwa Abdullahi Tundaga yarinta bai wuce kirkire kirkire ba Musamman a fannin na’ura Mai kwakwalwa inda yakaranta wannan fanni na kimiyyar na’ura Mai kwakwalwa yakuma fita da sakamako Mai kyau daga wannan makaranta

Bayan Kashif Inuwa Abdullahi ya kammala karatun digirinsa na farko yatafi bautar kasarsa inda yayi a kamfanin mulmula karafuna na ajaokuta,burinsa da sha’awarsa Kan neman ilmi yasa bai tsaya haka ba yacigaba da karatunsa a jamiar Harvard dake kasar amurka inda yakaranci fannin al’amuran shugabanchi daga bisani kuwa ya halarci cibiyar nazarin harkokin kimiyya dake masaschef Dan fadada nazarinsa akan harkokin fasahar zamani da kimiyyah Wanda duniya ke alfahari dashi a halin yanzu

Malam Kashif Inuwa Abdullahi bai tsaya hakaba inda yakuma halarci horo na Musamman a kasar India da hakan yabashi damar Zama samun shaida ta kwararre Kan al’amuran yanar gizo da ake Kira CCII,kammala samun horonsa a kasar India keda wuya kasashe daban daban irinsu hadaddiyar daular larabawa (UAE) kasar Kenya da ita kanta kasar India suka Nuna matukar bukatarsu na aiki dashi,to saide burinsa na ciyar da kasar haihuwar sa (nigeria) gaba ya hanashi amsa gayyatar da kasashen sukai masa.

A nigeria Kashifu Inuwa Abdullahi ya Fara aiki da cibiyar rarraba yanar gizo ta Galaxy ta kasa da ofishin ta dake Jihar haihuwar sa Jigawa Inda yarike mukamai daban daban tare da bada gudunmwar sa kasancewar kwararre a al’amuran fasahar sadarwa ta zamani,daga bisani babban bankin Nigeria (CBN) yabashi gurbi a shekara ta 2014 inda daga baya yakama aiki da Hukumar bunkasa cigaban fasahar sadarwa ta Nigeria wato (NITDA)

Hazakar aiki jajircewa kyawun Hali da kwarewa ta fuskar aiki yasake kulla alaka ta sama da shekara ashirin tsakanin sa da babban daraktan Hukumar na wancan lokaci malam ISAH ALIYU PANTAMI biyo Bayan zaben shekara ta 2019 aka ciyar da likkafar malam Isa Ali zuwa mukamin minister na sadarwa da bunkasa tattalin arziki ta fasahar sadarwa ta zamani na nigeria hakan ya Sanya zabar malam Kashif Inuwa Abdullahi a matsayin sabon babban director na Hukumar bunkasa cigaban fasahar sadarwa ta zamani ta nigeria

A shekara guda ofishin malam Kashif Inuwa Abdullahi ya cimma nasarori da dama Wanda suka zamo dorawa ne Kan nasarorin da shugaban sa Dr Isa Ali Pantami Yasamar, cigaban da malam Kashif Inuwa yake samarwa a Hukumar zaa iya cewa sun samo asali da irin cigaban Daya Samar tun a lokacin aikinsa a Babban bankin Nigeria (CBN) inda ya kirkiri na’ura Mai idon kyamara dake Aika sako lungu da sako da hakan ya inganta cikakken tsaro a bankin tare da Hana duk wani Mai muguwar manufa iya kaiwa ga bankin

Kashifu Inuwa Abdullahi yakuma Samar da wani Tsari na Musamman Kan na’ura Mai kwakwalwa da tasarrufin yanar gizo Daya taka rawa wajen aiwatar da tasarrufin kudade a hanyar yanar gizo a nigeria, karkashin shugabancinsa ya samarda Computoci da na’urori da sauran dama data Samar da aikin Yi ga miliyoyin alummar wannan kasa, tsakanin watan April zuwa karshen shekara ta 2018 a matsayin maaikaci a Hukumar bunkasa cigaban fasahar zamani ta nigeria malam Kashif Inuwa Abdullahi Yabada gudunmawa ta Musamman data temaka bunkasa tattalin arzikin nigeria inda tattalin arzikin kasar ya bunkasa da samada kaso goma Sha uku 13% inda hakan yacigaba da karuwa har zuwa shekara ta 2020 wadannan nasarori da aka cimma nada alaka da cigaban fasahar zamani da yasamar a dukkan sassa Daya Hadar da harkokin Noma Daya Temakawa manoma bunkasa yawa dakuma ingancin amfanin gonarsu

Hukumar ta NITDA karkashin jagoranci na Kashif Inuwa Abdullahi baya ga saukaka aiyukan Hukumomi na Gwamnati da harkokin kasuwani yakuma kaddamar da shirye shirye dasuka shafi matasa Kai tsaye bisa manufar Samar da aikin Yi a tsakanin su a dukkan fadin nigeria

Haziki jajirtacce Kuma masani Kan al’amuran fasahar sadarwa ba makawa ya gudanar da gagarumin aiki da zaa jima ana cin moriyarsa a Nigeria Taya murna ta tabbata da fatan alkairi ga babban daraktan Hukumar bunkasa cigaban fasahar sadarwa ta NITDA bisa cika shekara guda akan wannan KUJERA Allah ubangiji yacigaba da dafa masa yakareshi tare da bashi nasarori a al’amuran dayasa gaba na cigaban wannan kasa tamu ameen

©
Hassan Nakudu
CSM

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button