Labarai

Dokar NNPC Tasa Masu Shigo da Fetur Yanzu Bazasu Iya Shigo da Fetur Zuwa Najeriya ba

Spread the love

Abisa yadda abubuwa ke tafiya yanzu haka, alamu na nuna cewa wuraren ajiyar man fetur da aka shigo dashi ka iya zama fayau ba komai.

Tun bayan cire tallafin man fetur da akayi, NNPCL ta kawo sababbin dokoki wadanda suka sha bam bam dana da.

Sakamakon sabon tsarin da aka sanya na shigo da man fetur Najeriya, wanda ke cewa dole sai kamfani nada wuri na gugan wuri har naira biliyan goma kafin a sahalewa kamfani izinin shigowa da fetur.

Sabon tsarin da babban kamfanin mai na ƙasa NNPCL ya sanya domin bayarwa a yiwa kamfani dakon man a jirgin ruwa zuwa Najeriya kamar yadda jaridar The punch ta ruwaito.

Rahotanni sun nuna yadda da yawa daga cikin gidajen man fetur a Lagos, sun kulle ofisoshin su, sun daina saidawa abokan huldar su mai.

Rahotan na Punch yace, masu saro man fetur din su jibge, suna cikin halin la-ila-ha-hula-i sabida gaza haɗa N5b-N10bn na yin sabon oda daga NNPCL.

A cewar majiyar:

A yanzu haka, NNPCL nada isasshen man fetur data ajiye a Najeriya, kuma a wajen su muke siya, kafin nu gama shirin sayowa daga waje. Yanzu dole ne mu haɗa kuɗi biliyan biyar zuwa biyan goma, ya danganta da adadin odar ka kafin ka samu damar sayo fetur ɗin” inji majiyar mu”.

Mike Osatuyi, shine shugaban ƙungiyar masu sayo man fetur yace,  yawancin gidajen mai basu da mai ne saboda  tashin gwauron zabi da farashin man yayi.

A cewar sa, yanzu haka masu gidan mai suna biyan N22.5m da N23m domin siyan tankar mai guda, inda ya ƙarƙare da cewar, a 29 ga watan Mayu,  an sayi man fetur  N8m duk tanka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button