Dole ace da mijin iya baba…
Cikin daren nan a yanzu haka shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar All Progressives Congress APC yanzu haka suna cikin ganawa da Jagoran jam’iyyar na kasa, Bola Tinubu, a gidansa da ke Bourdillion a Ikoyi, Jihar Legas. Wata majiya ta fada wa SaharaReporters cewa Shugaban rikon kwarya na APC, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, ya jagoranci sauran mambobin kwamitin da suka hada da Sakatare, Sanata Akpan Udoedehe; Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, da gwamnan jihar Neja, Sani Bello, ne suka halarci taron. Majiyar ta ce taron an yi shi ne don tabbatar wa Tinubu cewa rushe kwamitin Ayyuka na Jam’iyyar ba wanda aka yi niyya bane. Kwamitin Gudanar da Jam’iyyar na kasa karkashin jagorancin Adams Oshiomhole ya wargaje makon da ya gabata Kwamitin Gudanar da Jam’iyyar na kasa a wani taron gaggawa da Shugaba Muhammadu Buhari ya halarta. Ana dai ganin wannan a matsayin cikas ga burin Tunibu na zama shugaban kasar Nageriya duba da jita-jitar da mutane ke cewa Tinubu kusancinsa da Oshiomhole.