Labarai

Dole Ne Duk Sabon IGP Na Kasa Da Za A Nada Ya Kasance Yana Da Kwalin Da Yafi Digiri Na Farko, Cewar Buhari.

Spread the love

Wata sabuwar doka da Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya sanya wa hannu, ta kara mafi karancin cancantar mukamin Sufeto-Janar na yan sanda.

Dangane da Dokar ‘Yan Sandan Najeriya ta 2020, duk wanda za a nada a matsayin IGP dole ne ya mallaki digiri na farko ko makamancin haka.

Sashe na 7 (2) na dokar ya karanta a wani sashi, Mutumin da za a nada a matsayin Sufeto-Janar na yan sanda zai kasance babban jami’in ’yan sanda ne da bai gaza matsayin Mataimakin Sufeto-Janar na Yan sanda ba.

Tare da cancantar karatun da bai kasa ba fiye da digiri na farko ko makamancinsa ban da kwararru da kwarewar gudanarwa.

Koyaya, abin da ake buƙata don zama Shugaban Najeriya yayi ƙasa da na IGP.

Jaridar punch wacce itace ta wallafa maganar da Shugaban Kasar yayi a shafukan sadarwar Zamani a yammacin yau.

Babi na VI, Kashi na 1, Sashe na 131 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce mutum na iya cancanta da zaben ofishin shugaban kasa idan dan asalin Najeriya ne ta hanyar haihuwa, ya kai shekaru 35 kuma ya sami ilimi har zuwa mafi ƙarancin matakin shedar makaranta ko makamancinsa.

Sashe na 131, wanda aka yi wa kwaskwarima a cikin shekarar 2018, ya karanta a wani sashi, mutum zai cancanci zaben shugaban kasa idan ya kasance dan Nijeriya ne ta hanyar haihuwa; ya kai shekara 40, memba ne na kungiyar siyasa kuma waccan kungiyar siyasa ce ke daukar nauyinsa, kuma ya sami ilimi har zuwa aƙalla matakin Takardar Makaranta ko makamancinsa.

Kudirin da ke neman mayar da babbar difloma ta kasa a matsayin mafi cancanta ga duk wanda ke son zuwa ofishin Shugaban kasa ko na gwamna ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Dattawa a watan Maris.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button