Labarai

Domin Ayyukan Cigaban Al’ummar Jihar Kaduna Sanata Uba Sani Yayi Sanadin samar da Bilyan 135.2Bn Ga jihar…

Spread the love

A cigaba da kokarin Samar da ayyukanyin matasa a jihar kaduna Sanata Uba Sani Yayi aiki tukuru ba dare ba Rana Don ganin gwamnatin Jihar kaduna ta samu lamunin Samun bashin Dolar Amurka Milyan dari uku da hamisin $350 Million Wanda yanzu haka darajar kudin ya zo daidai da Kudin Nageriya Naira Bilyan dari da talatin da biyar da Milyan dari uku da talatin da shida da dubu dari biyar N135,236,500,000.00
Wannan bashi Yana da matukar sauki ga hanyoyin biyansa Domin kuwa Jihar Kaduna Zatayi Shekaru arba’in 40 tana biyan bashin ba tare da takura ba, kenan gwamnatin jihar kaduna da al’ummar jihar ba zasu fuskaci ko wacce irin matsala ba balantana su shiga wani hali ba wajen biyan bashin.

Babban bankin Duniya (World Bank) da sauran hukumomin da Suka shafi al’amuran kudi na Duniya sun tabbatar da cewa jihar kaduna ta cancanci samun wannan bashin Bilyoyin Naira.

Masu karatu dai idan baku manta ba a lokacin Majalisa ta takwas 8 ne Gwamnatin jihar kaduna ta bukaci Majalisar ta amince mata domin karbon wannan bashi Amma Majalisar Sam Taki amincewa da Wagga Kudri na jihar kaduna. zuwan Sanata Uba Sani Majalisar ta dattijan Nageriya ne yasa Majalisar ta amince ta Kuma yarda da Wagga kudri na gwamnatin jihar kaduna sakamakon irin yadda sanatan ya bayyanawa Majalisar kyawawan manufar karbo wannan Rance inda sanatan ya bayyana irin manya manyan ayyukan alkharin da gwamnatin jihar ke so tayiwa al’ummar jihar ta kaduna da Kudin…

Ayyukan da gwamnatin jihar take so tayi da kudaden dai sun hada da Gina makarantun sakandiri inganta tsaro inganta fannin harkokin lafiya tare Samar da dubbannin ayyukan alkhari ga matasan na jihar kaduna.

Sanata Uba Sani Ya bayyana ya Kuma tabbatar da cewa gwamna Malam Nasiru El Rufa’i Zai ayyukan Cigaba na alkhari ga Al’ummar jihar kaduna da wannan Bilyoyin Naira da aka karbo daga Babban bankin Duniya…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button