Labarai

Domin fito da ku’din Haram da miyagu suka boye yasa muka fito da tsarin Chanja fasalin ku’di a lokacin zaben ~Cewar Buhari

Spread the love

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa aka bullo da manufar sake fasalin naira a lokacin zaben 2023.

Buhari ya bayyana haka ne a hirarsa ta farko tun bayan barinsa mulki, wadda aka haska a daren ranar Litinin a gidan talabijin na Najeriya (NTA).

Kuna iya tuna cewa babban bankin Najeriya, CBN, karkashin Gwamna Godwin Emefiele, ya aiwatar da tsarin sake fasalin kudin Naira da aka aiwatar, wanda ya tilastawa ‘yan Najeriya da dama shiga cikin kunci saboda karancin takardun kudi.

Shugaba Buhari yace an shirya hakan ne domin fito da ku’din da jama’a suka boye wanda suka kasance kudin Haram.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button