Labarai

Domin Kawo karahen Ta’addanci Za’a Gina Kwalejin Fasahar Gandun Daji A birnin Gwarin jihar kaduna..

Spread the love

Har’ila yau a Kokarin sa na samun Zaman lafiyar Al’ummar sa da cigaban jihar kaduna Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalissar Dattijan Nageriya Sanata Malam Uba Sani bayan Kudrin Kwalejin Garin Giwa Ya sake kai Kudrin Kirkirar Sabuwar Kwalejin Fasahar Gandun Daji Da Bincike, ( Federal College Of Forestry Technology And Research ) A garin Birnin-Gwari.
Karamar Hukumar Birnin Gwari dai kamar yadda kowa ya sani ne tana daya daga cikin garuruwan da suke fama da matsalar harin ‘yan ta’adda,  ‘Yan bindiga barayin shanu da masu garkuwa da mutane.
Bincike ya nuna bisa nazarin masananaduniya cewa tsaro da zaman lafiya bashi samuwa dole sai da ilimi, a halin da ake ciki yanzu bayarda ilimi ga matasa shine kadai zai kawo karshen matsalar wannan Ta’addanci da yake barazana da rayukan Al’umma a wasu garuruwa dake arewacin Nageriya Hakan yasa sanata Uba sani yasha alwashi tare da bayar da kansa ga al’ummar jiharsa da baki dayan arewa don ganin ya kawo cigaba tare da zaman lafiya mai dorewa arewacin Nageriya a bisa baiwar da Allah ya bashi.

Kudrin Kwalejin da sanata Uba sani Ya kai majalisa kawo yanzu haka dai Kudrin ya haure matakin karatu na biyu a Majalisar ta Dattijan ta Nageriya wanda yanzu haka ana gafda gayyatar jama’ar garin na Birnin-Gwari Zuwa Majalissar Dattijai Domin jin Ra’ayoyin su ( Public Hearing ), daga nan sai matakin saka  hannun Shugaban kasa, sai  fara aikin…
Samar da Manyan Makarantu domin wayarda kan matasa a garuruwan da suke fama da harin Ta’addanci shine abinda Bincike ya nuna zai iya samar da zaman lafiya ga Al’ummar…

Burin Sanata Uba Sani shine kawo karshen tashe tashen hankulan Ta’addancin jihar kaduna dama sauran wasu yankuna na Arewacin Nageriya…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button