Domin kubutar da ‘yan matan da aka sace Zamu taimaki Gwamna Matawalle ta ko Wacce hanya ~Inji Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya Girgiza da sace daliban jihar Zamfara inda Yace hakika Zuciyata ta yi nauyi matuka game da sace ‘yan matanmu’ yan matan Makarantar Sakandaren kwana ta gwamnati, da ke Jangebe, a Jihar Zamfara.
Na yi zantawa ta waya da Gwamnan Zamfara, H.E Bello Matawalle, kuma ya sanar da ni cewa gwamnatinsa na yin duk abin da za ta iya don ganin an sako daliban da aka sace.
Na gabatar da shawarwari a baya kan yadda al’ummarmu abin kauna za ta iya fatattakar makiya jihar kuma ta yi nasarar yaki da ta’addanci, kuma na tsaya kan wadannan shawarwarin.
Koyaya, a yanzu, dole ne dukkan hanunmu su goyi bayan gwamnatin jihar Zamfara wajen ganin an sako wadanda aka sace.
Gwamnatin Tarayya ba za ta iya tsammanin Jihohi za su samar da tsaro na rai da dukiya a yankinsu ba, ba tare da ba su iko kan tsaron cikin gida ba. Wannan yanzu larura ce.
Don haka, ina kira ga Majalisun Kasa da na Jiha da su fara aiwatar da garambawul ga tsarin mulki da shari’a wanda zai tabbatar da hakan. Dole ne majalisar dokoki ta jagoranci, domin da alama bangaren zartarwa ba zai iya samar da shugabancin da ake bukata ba kan wannan batun.
Zuciyata na tausaya wa dangin yaran da aka sace, kuma na mika hannun dama na zumunci ga Gwamna Matawalle, don taimakawa ta kowace hanya.