Labarai

Domin samar da gidaje miliyan 28m ga talakawan Nageriya muna bukatar ku’di Naira Tiriliyan 21tr ~kashim Shettima.

Spread the love

Mataimakin shugaban kasa, Sen. Kashim Shettima ya ce, duk da kokarin da gwamnatoci a matakai daban-daban suke yi, gibin gidaje a Najeriya na ci gaba da yin yawa, domin kuwa za a bukaci Naira tiriliyan 21 don cike gibin yadda ya kamata.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a Sokoto a wajen kaddamar da ginin rukunin gidaje 500 da gwamnatin jihar ta yi.

Sen. Shettima wanda ya yabawa gwamnan jihar, Ahmed Aliyu bisa kokarin da yake yi na magance bukatun gidaje na jama’ar sa, ya bayyana cewa gibin gidaje a Najeriya ya kasance babban kalubale.

A cewar VP, “Najeriya na da gibin gidaje miliyan 28 kuma za mu bukaci Naira tiriliyan 21 don biyan bukatun mu na gidaje.

“Wannan matakin da Gwamnan ya dauka abin a yaba ne matuka, kuma ya cancanci sauran gwamnatocin Jihohin su yi koyi da shi.

Ya kara da cewa, “Gwamnan ya fara da kyau ta hanyar kammala tituna da gadar sama da ya gada.

Tun da farko a nasa jawabin, gwamna Aliyu ya ce gidan na ma’aikatan gwamnati ne kuma za a sayar musu da su idan an kammala su bisa ga magidanta.

“Wannan wani aiki ne da tsohon Gwamnan Jihar, Aliyu Magatakarda Wamakko ya kaddamar amma daga baya gwamnatin da ta shude ta yi watsi da shi amma mun kuduri aniyar kammala shi domin amfanin ma’aikatanmu da sauran jama’a,” inji shi.

Gwamnan ya bayyana cewa aikin da ke karamar hukumar Wamakko zai lakume gwamnatin jihar Naira biliyan 7.3 domin kammala aikin.

Taron wanda zai cika kwanaki 100 akan karagar mulki da gwamnatin ta samu halartar tsohon gwamnan jihar Sokoto Sen. Aliyu Wamakko; Ministan Noma da Abinci, Abubakar Kyari; Karamin ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli Bello Goronyo da tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto Mukhtari Shagari da dai sauransu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button