Domin Sanya Idanu Akan Jami’an SARS, Hukumar Yan Sanda Ta Fitar Da Lambobi Kira Kai Tsaye, Ko Tura Saƙwanni.
A yanzu al’umma za su iya yin amfani da wadannan lambobi don shigar da koke da zaran jami’in FSAR ko wani jami’in rundunar ya ci zarafinsu
Idan ba a manta ba, Sifeta Janar na rundunar ‘yan sanda, ya dakatar da jami’an FSARS daga gudanar da wasu ayyuka sakamakon zarginsu da zaluntar mutane.
Lambobin wayar da kafofin sadarwar an samar da su ne domin baiwa al’umar damar shigar da korafe korafe idan jami’an rundunar FSARS ko TS su ka ci zarafin su.
Rahotanni sun bayyana cewa, rundunar ta samar da wadannan hanyoyin ne domin yin nazari da sa ido ga ayyukan sashen FSARS da sauran jami’an kwantar da tarzoma da ke cikin ta.
Sashen kula da huldodin jama’a na rundunar ‘yan sandan Nigeria ya samar da lambobin waya da kafofin dandalin sada zumunta da WhatsApp domin tabbatar da tsaftataccen aiki a rundunar.
Ga lambobin tare da adireshi Kamar Haka:-
07056792065 Kira/sakon SMS/whatsapp
08088450152 Kira/sakon SMS/whatsapp
08057000003 – Sakon SMS & whatsapp kawai
08057000002 – Kira zalla
Shafin yanar gizo: www.facebook.com/ngpolice
Email: [email protected]
Email: [email protected]
Shafin yanar gizo: www.facebook.com/ngpolice
Twitter: @PoliceNG_PCRRU Daga Comr Haidar Hasheem Kano