Labarai

Domin tattauna mataki na gaba A dai-dai lokacin da ya rage kwanaki takwas Ya mika mulkin jihar Kogi Yahaya Bello ya gana da Shugaba Tinubu.

Spread the love

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, CON, ya samu kyakkyawar tarba daga shugaban kasa, Ahmed Bola Tinubu, GCFR, a fadar shugaban kasa dake Villa Abuja a ranar Juma’a inda ya gana da shugaban kasa.

Ganawar da gwamnan ya yi da maigirma shugaban kasa, an gudanar da tattaunawa mai zurfi da fahimta, inda aka zurfafa kan muhimman batutuwan da suka shafi tsaro da tattalin arziki.

A yayin wannan muhimmin taro, Gwamna Yahaya Bello ya samu yabo daga mai girma shugaban kasa, Tinubu bisa kyakkyawan jagoranci da ya nuna wajen tafiyar da jirgin ruwan jihar Kogi tun bayan hawansa mulki a watan Janairun 2016.

Wannan karramawar da shugaban kasa ya bayar ya zama shaida ga shugabancin Gwamna Bello na abin yabawa, tare da tabbatar da jajircewarsa da bayar da gudunmawa mai tasiri wajen ci gaban al’ummar jihar Kogi.

A ranar 27 ga watan Junairu, 2016, wa’adin Gwamna Yahaya Bello zai kare a ranar 27 ga watan Janairu, 2024 domin zai mika ragamar mulki ga wanda ya cancanta, Ahmed Usman Ododo, zababben gwamna.

Wannan na kun she ne a cikin wata sanarwar ONOGWU Muhammad
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button