Labarai
Don Saukaka Tsadar Abincin Dabbobi, Shugaban Buhari Ya Amince Da Sakin Tan 30,000 Na Masara Daga Ma’ajiyar Gwamnati..
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aminci da fito da tan 30,000 na Masara daga dakin adana kayayyaki na gwamnati don saukakawa masu hada abincin Dabbobi.
Shugaban ya fadi hakan ne a shafinsa na Twitter.
Yace “Don sauƙaƙa tsadar da ake samu yanzu na noman kaji, Na amince da sakin tan 30,000 na masara daga m’ajiyar ƙasa, ga masu samar da abincin dabbobi.”
Yanzu haka a halin da ake ciki a Najeriya kayan abin ci da kayayyakin amfanin yau da kullum duk sunyi tsada.
Daga Sabiu Danmudi Alkanawi