Don Tsira Da Rayuwarmu Da Barazana Da Tashin Hankalin Da Muka Shiga Ne Yasa Muka Bayyana Sakamakon Zaben Jihar Taraba Ba Tare Da Mun Bincika Ba, Duk Da Magudin Da Aka Tafka A Zaben – Baturen Zabe Ya Sanarwa Da INEC
Kamar yadda za ku gani a cikin wannan takardar dake kasa shugaban jami’ar kimiya da fasaha ta Tarayya Abubakar Tabawa Balewa University dake jihar Bauchi Prof. M A Abdulaziz ya rubuta tun a ranar 23 ga wannan watan na Maris, wanda shine Baturen zaben da ya jagoranci zaben jihar Taraba a zaben Gwamnoni da ya gabata.
A cikin rubutun nashi ya tabbatarwa da INEC da cewa Hatsaniya da aka samu tsakanin jami’an tsaron Sojoji da na ‘yan sanda masu tsaron cibiyar sanar da sakamakon zaben ya kawo jinkiri da fargaba a aikin gabatar da sakamakon. Ya kuma tabbatar da cewar saboda matsi, fargaba da tashin hankalin da suka fuskanta, shi ya tilasta musu sanar da sakamakon zaben a yadda aka kawo musu ba tare da bin ka’ida ba don tsira da rayuwarsu.
Sannan ya karbi korafi daga jam’iyyar NNPP akan yadda aka gudanar da aikin zaben a wasu kananun hukumomi, da yadda akayi aiki da BVA’S da I-REV na tafka mummunan magudin zabe da kara yawan kuri’u.
Wannan korafin da Baturen zaben ya gabatar kadai ya tabbatarwa da Duniya cewa lallai dan takarar NNPP Farfesa Muhammad Sani Yahaya ne ya lashe zaben da gagarumin rinjaye.
Dalilin wannan korafin yasa Hukumar INEC dake Abuja da kanta ta jagoranci REVIEW na zaben jihar Taraba kuma ta tabbatar da mummunan magudin da aka tafka mai yawan gaske, wanda a yanzu haka sun kammala Review din zaben jihar baki daya sauran kawai su sanar da halin da ake ciki da kuma hukuncin da za’a yanke, sai mu cigaba da Addu’a Allah Ubangiji ya cigaba da tona musu asiri.
Tun lokacin da aka fara review din zaben munafukan jihar Taraba suka tare a Abuja suna ta bin kafa har fadar shugaban kasa da wurin Sarkin Musulmi sunje duk don a bar binciken amma bukatarsu bata biya ba, kuma Insha’Allahu sai sun wulakanta.
‘Yan uwana muyi hakuri kada mu zagi Baturen zaben nan domin shima abun yafi karfinshi shiyasa sai da ya samu ya gudu daga jihar sannan ya sanarwa da INEC halin da ake ciki, na tabbata inda wani ne ko ina yaje bazai sanarwa da INEC abunda ya faru ba saboda gudun abunda ka iya faruwa a nan gaba musamman a wannan lokacin na rashin tsaro.
Hakika Addu’armu tayi matukar tasiri, Insha’Allahu zamu ji Alkhairi nan bada dadewa ba.
Daga Comrd Abba Pantami