Dr Pantami ya Mika Wasikar yabo ga sa’adat Wacce ta samar da manhajar Rahotan Fyade.
A madadin Gwamnatin Tarayyar Najeriya a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari GCFR, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami FNCS, FBCS, FIIM a yau a hukumance sun gabatar da wasikar yabo ga Wacce ta kirkiro Shamrock Innovation Hub, Miss Sa’adat Aliyu.
Yabon ya kasance ne bisa la’akari da manhajar da Miss Aliyu ta kirkira, (Helpio App) wacce ke da nufin taimakawa wajen bayar da rahoto game da cin zarafin mata. An gabatar da Miss Aliyu a hukumance tare da wasikar a wani takaitaccen bikin da aka gudanar a Cibiyar Sadarwa da Tattalin Arziki ta Digital, Abuja.
Mai girma Ministan, Dakta Pantami ya kara umurtar Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA) da ta yi hulda da matasan da za su fara sana’ar, su ba ta shawara, su sa ido kan ci gabanta tare da tallafa wa tsarin a karkashin yadda dokar ta tanada.
Ministan, Dakta Pantami ya yaba da shirin, yana mai jaddada cewa kirkirar fasahar sadarwa ta zamani da kuma kasuwanci shi ne hanya ta ci gaba wajen samar da arziki da samar da hanyoyin magance matsalolin da suka shafi al’umma.